ABNA24 : Shafin yanar gizo na labarai mai suna ‘Hail” ya nakalto Landerking yana fadar haka a yau Laraba, a ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka.
Wannan jami’an diblomasiyyar kasar ta Amurka ya burus ta mummunan halin da mutanen kasar Yemen suke cikin saboda killacewa da kuma hare-haren da saudiya da kawayenta suke kaiwa kan mutanen kasar ta Yemen, sannan ya tuhumi kasar Iran da tallafawa kungiyar Ansarallah da horaswa da kuma makamai.
Tun ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2015 ne kasashen saudiya da UAE da wasu kawayensu suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar.
A halin yanzu an shega shekara ta 7 kenan ba tare da sun cimma wannan burin ba.
342/